<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Muna Zuwa Wurin Yesu, Mai Ceto LW265</title>
<lyrics>[V1]
 1) Muna zuwa wurin Yesu, Mai Ceto,
 Don mu shiga aikinsa.
 Shi ya kira mu mu yi ta wa'azi
 Ko'ina a duniya.

[V2]
 KORUS
 Yesu ne Shugaba,
 Shi ne mai ƙaunar mutane.
 Za mu taya shi nemansu
 Don su sami gafara.

[V3]
 2) Komenene Yesu shi ya ce mu yi,
 Za mu yi da zuciya ɗaya.
 Za mu yi biyayya cikin abu duk,
 Za mu yi ta wa'azi
 Korus

[V4]
 3) Shi ya ce mu bar duk zunubai na dā,
 Mu tafi da tsabtar rai.
 Ko ya nemi kayan da ke wurinmu,
 Za mu ba shi nandanan.
 Korus

[V5]
 4) Sai mu yi aniya cikin aikinsa
 Sai mu ƙara ƙoƙari.
 Shi da kansa zai tafi tare da mu
 Har iyakar duniya.
 Korus</lyrics>
<hymn_number>265</hymn_number>
</song>